Allah ya yi wa Ibrahim Musa Argungu rasuwa ranar Lahadi 2 ga watan Oktoba 2022.
Kafin rasuwarsa ya taba aiki da Kamfanin karafa na Ajaokuta, daga bisani ya yi aiki da Gwamnatin jihar Kebbi a matsayin S.A Media ga Gwamnan jihar Kebbi na waccan lokaci Saidu Nasamu Dakingari.
Ibrahim kane ne ga Muhammad Musa Argungu Tambarin Kabi
Ya rasu ya bar mata biyu da yara biyu.
An yi Jana'izarsa ranar Litinin 4 ga watan Oktoba da karfe 10 na safe a Kaduna.
Allah ya jikansa ya gafarta masa.
Rubuta ra ayin ka