Abin da ya sa dillalan motoci ke tunanin an kara kudin fiton shigar da motoci Najeriya


Hukumar kwastam a Najeriya ta yi karin haske kan abin da ya sa ake ganin harajin shigo da motoci ya karu a kasar.

BBC ta ruwaito Shugaban hukumar, Kanal Hamid Ali mai ritaya a wajen wani taron manema labarai a fadar shugaban kasa ya ce sam hukumarsu ba ta yi karin komai ba kan kudin fitonsu.

Kalaman nasa na zuwa ne yayin da dillalan motoci da masu sayensu a Najeriya ke kokawa kan karuwar harajin shigo da motocin cikin kasar inda har wasu bayanai ke cewa yanzu wasunsu sun koma shigowa da wadanda aka yi hadari da su suna gyarawa.

A tattaunawarsa da BBC, Kanar Hamid mai ritaya ya ce abin da ke janyo hauhawar kudin fito shi ne faduwar darajar naira a kan dala. "Sai mutum ya ce an kara, ba a kara ba, saboda naira ce da ta fadi,"

Na biyu kuma batun cuwa-cuwa da ake yi da, ba a biyan ainahin harajin da ya kamata a biya, yanzu da muka sa wannan na'ura yana tabbatar mana da ranar da aka yi motar - shekararta daya ne ko biyu ne ko uku ne, ana samun diddigin kudin da ya kamata a biya, yanzu mutane suna biyan kudin da ya kamata su biya." in ji shugaban hukumar ta kwastam

Da yake magana kan batun kasa biyan kudin haraji domin fitar da motoci da ke jibge a tashoshin jiragen ruwan Najeriya kuwa, shugaban kwastam din ya ce "doka ta bamu dama idan suka kai kwanakin da ya kamata a wurin nan ba ka fitar ba, akwai abin da ake kira "overtime cargo", gwamnati ta ce mu kwasa, idan muka ajiye ba ka je ka biya ba, shi ke nan sai mu je mu dauka mu saida."

Kan batun rufe iyakoki da zargin shigar da wasu kayayyakin da aka haramta kuwa, Kanal Hamid Ali mai ritaya cewa ya yi duk wani abu da aka shigo da shi, ta ruwa, ta kasa ko ta sama, sai ya zamana yana cikin dokar kasa.

Ya ce kayan shaye-shaye da bindiga da gwanjo da shinkafa suna cikin abubuwan da gwamnati ta haramta shigowa da su cikin kasar

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN