Zan iya mutuwa kafin ki', Bidiyon karshe na 'yar Kano wanda wani masoyinta dan kasar China ya kashe, kalli bidiyon

'Zan iya mutuwa kafin ki', Bidiyon karshe na 'yar Kano wanda wani masoyinta dan kasar China ya kashe


A ranar Juma’a, 16 ga watan Satumba, kisan da ake zargin wani masoyinta dan kasar China ne ya yi wa Ummakulsum Sani Buhari a jihar Kano ya tayar da hankula a bangarori daban-daban.

Sai dai kuma, bayan kwana biyu da kisan gillar, wani faifan bidiyo mai tada hankali da ke nuna matar da aka caka mata wuka ta bayyana a shafukan sada zumunta.

Wani faifan bidiyo a intanet ya nuna matar mai shekaru 23 da nuna farin ciki yayin da take hira da wata kawarta da ba a tantance ba.

Ummita kamar yadda kawaye da ’yan uwa suka kira ta cikin jin dad’i sai aka ga ta gayawa kawarta wacce ta kira Saurauniyya cewa ta mutu kafin ta.

Kalaman Ummita:

“Sarauniya zan iya mutuwa kafin ki; kowa yana da nasa makoma kuma yana zuwa ba tare da an sanar da shi ba. Zan iya barci yau kuma ban farka ba (mutu).

"Mu mutu da imani ba za ki mutu ki bar ni ba har sai kin haifi 'ya'ya ashirin."

Amma a martaninta, Saurauniyya ta yi sauri ta shiga ciki tana tsawatar kawarta cewa ba za ta mutu ba.

Ta ce:

“Zan mutu kafin ki mutu; a'a, zan mutu kafin ki. Ba za ki mutu ba sai kin haifi ‘ya’ya hamsin, hhhhhhh”.

A karshe abokanan biyu sun kwashe da dariya bayan gajeriyar tattaunawar da suka yi kan al'amuran mutuwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN