An kama wani matashi mai shekaru 28 da haihuwa mai sana’ar sayar da maganin gargajiya da laifin satar kan gawa da hanjin wata mata a makabartar Musulmi, Oke Yidi, a Ede, jihar Osun. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
An kama Ismail Adewuyi ne a ranar Asabar, 17 ga watan Satumba, daga hannun mafarauta da tsaron dazuka.
Adewuyi wanda ke dauke da laya, ya kai hari a makabartar da sanyin safiyar Asabar. Sannan ya tono wata gawa, ya yanke kai, ya fito da hanjin cikinta.
Sai dai wani ma’aikacin mafarauta wanda ya dauki yunkurin Adewuyi a matsayin abin tuhuma, ya kama shi a lokacin da yake fitowa daga makabarta.
Mafarautan sun gano kan gawar da hanjin da aka yanke a hannun Adewuyi inda suka mika shi ga ‘yan sanda.
Ana ci gaba da gudanar da bincike.