Yiwuwar hana cin ganda: Har Kotu zamu kai FG idan ta hana talakan Najeriya cin naman ganda "ponmo" - Lauya dan kudu

Yiwuwar hana cin ganda: Har Kotu zamu kai FG idan ta hana talakan Najeriya cin naman ganda "ponmo"  - Lauya dan kudu


Tsohon Shugaban Kungiyar Lauyoyin Najeriya reshen Ikeja (NBA), Dokta Monday Ubani, a ranar Laraba ya roki Gwamnatin Tarayya ta bari yan Najeriya su ci gaba da cin fatar dabbobi da ake kira “Ponmo” watau ganda. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Ubani ya yi wannan roko ne a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Legas, biyo bayan abin da ya bayyana a matsayin barazanar hana cin fatar dabbobi.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa, a kwanakin baya ne Gwamnatin tarayya ta ce tana gabatar da wata doka da za ta hana cin fatun dabbobi domin farfado da masana'antar fatu.

Duk da haka, Ubani ya ce "ponmo" ko Kuma ganda, wani muhimmin abu ne a cikin abincin yau da kullum na yawancin 'yan Najeriya.

Ya ce hana cin ta na iya zama da wahala ga masu cin ta.

A cewar Ubani, wanda shi ne Shugaban Hukumar NBA Sashen Ra’ayin Jama’a da Ci Gaban Dokar (SPIDEL), sashin zai nemi kariya daga kotu, idan aka aiwatar da wannan haramcin. 

Ya ce ganda, watau “ponmo” an yi la’akari da shi a matsayin abincin talaka kuma talakawan Najeriya suna ji daÉ—insa.

Ya ce hana cin ta na iya haifar da damuwa ga talaka

“Kayan abinci da ake kira ponmo shi ne abincin da talakawan kasa ke ci saboda arharsa, ganin cewa kifaye da nama da sauran abubuwan gina jiki sun yi tsada sosai kuma talakawa ba sa iya samun su.

"Gaskiya ita ce ponmo (ganda) ya kasance mafi yawan furotin ko sinadari mai kama da nama a cikin miyan gidan kowane talaka," in ji shi.

Ubani ya bukaci gwamnati da ta sake duba matakin da ta dauka domin kada a jefa talaka cikin wahala.

A cewarsa, miliyoyin 'yan Najeriya suna ganin "ponmo" watau ganda, yana da matukar dadi, musamman ya kasance abu ne mai araha wanda ke da kamannin nama ko kifi. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN