Ana zargin cewa wani saurayi mai suna Musa David ya kashe kanshi a hannun hukumar NSCDC a garin Birnin kebbi ranar Lahadi 11 ga watan Satumba 2022.
Wani Dattijo mai suna Mr. Augustine, wanda mamacin ke zaune tare da shi a gidansa da sauran yara suna karatu a Waziri Umaru Federal Polytechnic Birnin kebbi, ya shaida wa shafin labarai na isyaku.com cewa:
" Kwana uku da suka wuce yaron ya dawo gida yana yin wasu halaye da basu dace ba. Wanda ya haifar da zargin abin da ya faru da shi. Sakamakon haka aka kira wani makwabcinsu wanda jami'in NSCDC ne ya tafi da shi ofishinsu tun shekaran jiya".
"Sai dai kwatsam sai aka kira ni (Mr. Augustine) aka shaida mani cewa Musa yana Asibitin Sir Yahaya a garin Birnin kebbi.
Shafin isyaku.com ya samo cewa Musa David yana raye lokacin da aka isa da shi asibiti har ya yi wa Likita wasu bayanai. Sai dai daga bisani ya mutu.
Kakakin hukumar NSCDC na jihar Kebbi ya shaida wa shafin isyaku.com cewa shi baya da Labarin aukuwar lamarin. Sai dai ya yi alkawarin cewa zai bincika kuma zai tuntube mu. Kawo lokacin rubuta wannan labari bai waiwaye mu ba.
Sakamakon binciken hukumar NSCDC na jihar Kebbi ne kadai zai iya tabbatar da inda lamarin ya faru da hakikanin abin da ya faru kafin mutuwar Musa David.