Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari kan ayarin motocin Sanata, sun kashe hadimai (hotuna/bidiyo)


Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari kan ayarin motocin Sanata Ifeanyi Ubah a unguwar Enugwu-Ukwu da ke karamar hukumar Njikoka a jihar Anambra a ranar Lahadi 11 ga watan Satumba, inda wasu da ba a tantance adadinsu ba suka mutu. Shafin isyaku.com ya samo.

‘Yan bindigar sun bude wuta kan ayarin motocin da yammacin Lahadi. Jami’an ‘yan sandan da ke cikin ayarin motocin sun mayar da martani kan harin amma abin bakin ciki an kashe wasu da dama daga cikinsu a arangama da aka yi.

Sanatan ya yi nasarar tserewa duk da cewa motarsa ta sha ruwan harsasai.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga ya tabbatar da cewa an kai hari kan jami’an rundunar a Enugwu-Ukwu, amma ya ce har yanzu ba a san adadin wadanda suka mutu ba.

''Kwamishanan 'yan sandan jihar Anambra CP Echeng Echeng ya jagoranci jami'an tsaro ranar 11/9/2022 zuwa wajen da aka yi harbe-harbe a Enugukwu. 

Ko da yake har yanzu ba a kayyade cikakken bayanin lamarin ba, jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da ayyuka kuman bincike kuma ana sa ido kan lamarin.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN