Yan sandan jihar Kebbi sun damke mutum 3 bisa zargin yi wa saurayi dukan ajali a Unguwar Badariya, Birnin kebbi bisa zargin satar babur


Rundunar yan sandan jihar Kebbi ta kama wasu matasa uku bisa zargin lakada wa wani saurayi mugun duka har ya mutu a Unguwar Badariya da ke garin Birnin kebbi bisa zargin satar babur. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Sanarwar haka na kunshe a wata takarda ta Kakakin hukumar Yan sandan jihar Kebbi SP Nafi'u Abubakar ya raba wa manema labarai ranar 23 ga watan Satumba a garin Birnin kebbi.

SP Nafi'u Abubakar ya ce:

"A ranar 19 ga Satumba, 2022 da misalin karfe 4:00 na safe, wani Abubakar Ahmed, Ubaidu Ahmed da Halilu Ahmed da ke unguwar Badariya, a Birnin Kebbi, suka hada baki suka je gidan wani Sanusi Abubakar ‘m’ mai adireshi daya, suka neme shi. ya kirawo musu kaninsa mai suna Abbas Abubakar AKA Zabi, domin suna zarginsa da sace musu babur, Haojue Roba-Roba". 

"Da  aka kira Abbas Abubakar, sai wadanda ake zargin suka kai shi gidansu, suka daure shi da igiya, suka yi masa dukan tsiya. A daidai wannan rana da misalin karfe 2:30 na rana, wadanda ake zargin sun tafi da Abbas Abubakar a cikin motarsu zuwa hedikwatar ‘yan sanda da ke Birnin Kebbi. Don haka nan take aka kama su, aka garzaya da Abbas Abubakar asibitin tunawa da Sir Yahaya da ke Birnin Kebbi, inda wani Likita ya tabbatar da rasuwarsa".

"Dangane  da abin da ya gabata, Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kebbi, CP Ahmed Magaji Kontagora ya umurci DPO da ya gaggauta mika karar zuwa SCID, Birnin Kebbi domin gudanar da cikakken bincike da nufin gano al’amuran da suka dabaibaye wannan ta’asa".

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN