Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 6 a wani hatsarin motar daukar kudi na Banki a jihar Kebbi

Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 6 a wani hatsarin motar daukar kudi na Banki a jihar Kebbi


Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutane shida da suka hada da ‘yan sanda uku a wani hatsarin da ya afku a ranar Talata a kan hanyar Argungu zuwa Birnin Kebbi a jihar.

Kakakin Rundunar SP Nafi’u Abubakar ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Laraba a Birnin Kebbi.

“Hatsarin ya faru ne a lokacin da wata mota kirar Carina E dauke da jarkokin man fetur daga zuwa Æ™auyen Jeda, motar Carina E ta yi karo da motar Bullion na Banki, a sakamakon haka, ta fashe da wuta tare da cinye wasu motoci uku.

“Saboda haka, jimlar motoci biyar da babur daya sun kone kurmus.

“Mutane shida da suka hada da ‘yan sanda uku kuma sun mutu a gobarar, yayin da wasu mutane biyar da ‘yan sanda uku suka samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kebbi domin kula da lafiyarsu,” inji shi.

Nafi’u ya ce kwamishinan ‘yan sanda Ahmed Magaji-Kontagora ya ziyarci inda hatsarin ya faru.

“Ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki da Ya ba wa rayukan da suka rasu hutu na har abada, ya kuma baiwa iyalansu kwarin guiwar jure wannan rashi mara misaltuwa.

"Magaji-Kontagora yana kuma tabbatar wa da jama'a cewa za a gudanar da cikakken bincike don gano abubuwan da suka faru a cikin mummunan lamarin," in ji shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN