An gurfanar da wani Darakta gaban Kotu a Sokoto kan badakalar N1.3m

An gurfanar da wani Darakta gaban Kotu a Sokoto kan badakalar N1.3m


Wata babbar Kotun tarayya da ke zamanta a Sokoto a ranar Laraba 28 ga watan Satumba, ta tasa keyar wani Darakta a hukumar kula da kayayyaki ta jihar Sokoto, Hassan Bello, a gidan gyaran hali bisa zargin badakalar naira miliyan 1.3.

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta gurfanar da Bello a gaban kotu bisa tuhuma guda daya da ya shafi zamba. An yi zargin cewa ya aikata laifin ne a wani lokaci a watan Agustan 2021.

Lauyan masu shigar da kara, Mista Hannafi Sa’ad ya shaida wa Kotun cewa Bello wanda Darakta ne na gudanarwa a hukumar, ya karbi kudaden ne daga hannun Aliyu Adamu-Tsaki, Yusuf Abubakar da Yahaya Salihu a gaban wani Dahiru Muhammad a Sokoto.

Sa’ad ya shaida wa kotun cewa ya gabatar da wasikun karya ga wadanda abin ya shafa wadanda daga baya aka gano na karya ne kuma babu su.

Yayin da Lauyan wanda ake tuhuma, Mista Aminu Mustapha, ya gabatar da bukatar neman beli a madadin wanda yake karewa, Lauyan mai shigar da kara ya nemi karin lokaci domin nazarinsa.

Mai shari’a Ahmad Mahmud wanda ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 4 ga Oktoba, 2022 don sauraron bukatar neman beli tare da ci gaba da shari’ar, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali da ke jihar har zuwa lokacin da aka dage sauraron karar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN