Wasu yara biyu masu shekaru 5 da 9 sun yi yunkurin sace wani yaro dan shekara 2 a jihar Kwara

Wasu yara biyu masu shekaru 5 da 9 sun yi yunkurin sace wani yaro dan shekara 2 a jihar Kwara


Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta fara gudanar da bincike a kan yunkurin sace wani yaro dan shekara 2 da wasu yara biyu masu shekaru 9 da 5 suka yi a Ilorin. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

An tattaro cewa an kama yaran ne a kasuwar Oja Tuntun, Baboko, cikin babban birnin Ilorin.

An yi zargin cewa kananan yaran sun yi yunkurin sace yaron ne a lokacin da ‘yan kasuwar da suka yi shakkun tafiyarsu, suka tayar da hankalinsu wanda ya kai ga kama su.

Wata majiya a kasuwar, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Nigerian Tribune cewa yaran sun yi ikirari cewa an yi musu alkawarin Naira 12,000 kowannensu idan sun yi nasara a aikin.

Majiyar ta kara da cewa, "Amma yanzu batun ya dauki wani sabon salo domin wadanda yaran suka ambata na alaka ne da mai jaririn.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce yaran da ake zargin sun ce suna kokarin gano iyayen yaron ne kawai. 

“Eh, muna sane da lamarin. Takaitaccen bayani da muke da shi yanzu shi ne, ya shafi yaro da yarinya ‘yan shekara 9 da 5, wadanda ake zargi da yunkurin sace wani yaro dan shekara biyu. Ya ce jaririn ya ɓace kuma suna ƙoƙarin gano iyayen," in ji PPRO. 

Ya kara da cewa, "Wannan shi ne bayanan da muke da su a yanzu amma ana ci gaba da bincike. Kuma idan aka yi la'akari da shekarun bangarorin da abin ya shafa, CP ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN