Ta faru: EFCC na iya kulle asusun Gwamnatin jihohin Najeriya – Kotun daukaka kara ta yanke hukuncin


Kotun daukaka kara ta tarayya, reshen Makurdi, ta yi fatali da hukuncin da babbar kotun tarayya, Makurdi ta yanke, da ke daure wa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta’annati, EFCC, daskarar da asusun Gwamnatin jihar Benue domin gudanar da bincike, ba tare da umarnin Kotu ba. Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

A wani hukunci na bai daya da mai shari’a MS Hassan ya yanke a ranar Alhamis, 22 ga watan Satumba, 2022, Kotun daukaka kara ta ce, EFCC na da ikon sanya duk wani asusu, (asusun Gwamnatocin jihohi) akan PND na tsawon awanni 72, domin gudanar da bincike. ba tare da umarnin Kotu ba. Kotun ta kuma yi watsi da diyyar Naira miliyan 50 da karamar Kotun ta yi wa EFCC.

Mai shari’a Mobolaji Olajuwon na babbar Kotun tarayya, Makurdi, ya yanke hukunci a ranar Talata, 2 ga watan Fabrairu, 2019, inda ya hana EFCC sanya PND a asusun Gwamnatin jihar Benue. Bata gamsu da hukuncin ba, hukumar ta garzaya Kotun daukaka kara.

Lauyan EFCC, Steve Odiase, ya zayyana kwararan hujjoji kan hukuncin da aka yanke a baya, kuma Kotun daukaka kara ta ce EFCC ta yi aiki da karfin da ta ke da shi na kulle asusun Gwamnatin jihar Benue.

Kotun ta kuma bayyana cewa, a bisa doka, dole bankunan su bi umarnin hukumar EFCC kan PND.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN