Mista Ibrahim Farinloye, Ko’odinetan shiyyar Kudu maso Yamma, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na NAN, afkuwar lamarin a ranar Lahadi a Legas.
Farinloye ya ce ginin da ke kan titin Oba Idowu Oniru, Lekki, ana kan gina shi ne a lokacin da ya ruguje.
Ya ce da alama mutane shida sun makale a karkashin baraguzan ginin.
Wadanda suka kai daukin gaggawa sun hada da rundunar ‘yan sandan Najeriya, NEMA da kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA).
Ana ci gaba da gudanar da ayyukan agaji kawo lokacin rubuta wannan rahoton.