Majalisar dokokin jihar Neja ta bayar da umarnin dakatar da shugabannin kananan hukumomi 15, duba dalili

Majalisar dokokin jihar Neja ta bayar da umarnin dakatar da shugabannin kananan hukumomi 15


Kwamitin Majalisar dokokin jihar Neja da aka kafa domin binciken basussukan kudaden kwangila na kananan hukumomi ashirin da biyar, ya bada shawarar dakatar da shugabannin kananan hukumomi goma sha biyar.

Shugaban kwamatin, Abdulmalik Madaki Bosso ya ce matakin dakatar da shugabannin karamar hukumar zai ba da dama ga mambobin kwamitin su samu damar gudanar da ayyukansu cikin lumana.

Shugabannin kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da na Mokwa, Gbako, Suleja, Gurara, Tafa Paikoro, Bosso, Agwara, Borgu, Kontagora, Wushishi, Magama, Mariga, Mashegu, da Rijau.

Ya ce hakan ya yi daidai da tanadin sashe na 128 da na 129 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima da kuma tanadin sashe na 90 karamin sashe na daya AB da C na kananan hukumomi 2001 da aka yi wa kwaskwarima.

Ya yi zargin cewa galibin shugabannin kananan hukumomin da aka dakatar sun karbi rancen ne ba tare da bin ka’ida ba, matakin da ya ce Majalisar dokokin jihar Neja ba ta amince da shi ba.

A cewarsa, matsalar ta kara wani nauyi a kan tafiyar da harkokin kananan hukumomi a jihar.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito Abdulmalik Madaki Bosso ya kara da cewa an dakatar da cire N8m kowacce daga kananan hukumomi domin biyan lamuni saboda gazawar ma’aikatar wajen samun kudirin gida kamar yadda sashe na 97 karamin sashe na daya na kananan hukumomin 2001 kamar yadda aka gyara.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN