Madalla: Tubabbun ‘yan bangar siyasa sun yi wani abin burgewa da zai ba ka mamaki a Zamfara

Tubabbun ‘yan bangar siyasa sun mika makamai, sun rungumi zaman lafiya a Zamfara


Wasu gungun Yan bangar siyasa guda biyu a Zamfara sun rungumi zaman lafiya tare da yin kira ga Gwamnatin jihar da ta yi amfani da su yadda ya kamata domin bayar da gudunmawa ga ci gaban al’umma.

NAN ta ruwaito cewa ‘Yan kungiyar sun ce sun yi nadamar yadda wasu ‘yan siyasa ke amfani da su wajen tayar da zaune tsaye a kan ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba.

Kungiyoyin karkashin jagorancin Baba Karami da Garba Lawal, wanda aka fi sani da Vice, sun ce sun koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma za su goyi bayan kokarin Gwamnati na maido da zaman lafiya a jihar.

Wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Zamfara, Yusuf Idris, ya rabawa manema labarai a ranar Litinin a Abuja, ya ce mambobin kungiyoyin sun mika makamansu ne domin nuna aniyarsu ta samar da zaman lafiya.

‘Yan kungiyar da makamansu sun samu tarba daga tsohon shugaban karamar hukumar Gusau, Alhaji Babangida Abdullahi, inda ya yi alkawarin mika makaman ga jami’an tsaro.

Makaman sun hada da wukake, sanduna da adduna.

Karami da Lawal dai sun ce tuban nasu ya biyo bayan fahimtar da suke yi cewa yayin da suke bata rayuwarsu ta hanyar kare muradun wasu ‘yan siyasa, ‘ya’yan irin wadannan ’yan siyasar na makaranta suna shirin samun kyakkyawar makoma.

Sun yi alkawarin hada kai da Gwamnatin jihar karkashin Gwamna Bello Matawalle domin ci cigaban jihar.

A nasa bangaren, Abdullahi ya yaba musu bisa yadda suka rungumi zaman lafiya tare da yin alkawarin bayar da gudunmawar ci gaban Zamfara.

Ya kuma ba su tabbacin cewa za a yi musu daidai da sauran ‘yan jam’iyyar APC, ya kuma bukace su da su ci gaba da bin doka da oda.

Abdullahi ya ce Gwamnatin Matawalle ba za ta amince da duk wani nau’in ‘yan daba ba, musamman yadda Gwamnati ke yaki da ta’addanci domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN