Karin bayani: Duba dalili da ya sa dan kasar China ya kashe budurwarsa a Kano


Mr. Geng dan kasar china da Ummukulsum Buhari sun yi soyayya,amma daga bisani ya sami labarin tayi aure (kamar yadda ya fada). Nasiru Salisu Zango ya ruwaito.

Don haka yayi fushi yaje gidanta ya kashe ta a unguwar su dake Jan bulo, kuma aka kai ta asibitin UMC anan tace ga garinku nan.

Ummukulsum ne sunan ta amma an fi kiran ta da Ummita ,ta gama digiri a fannin aikin gona daga jami’ar Kampala dake Uganda yanzu haka tana bautar kasa a Sokoto.

Jami’an immigration da yansanda ne suka kwace shi daga mutanen da suka fara dukanshi a unguwar ta Jan bulo kusa da layin Lawan Kyankyan.

Yanzu haka yana hannun yansanda 

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN