Jami’an VIO sun jikkata a wani hatsarin mota bayan sun biyo titi "hannu daya" yayin da suke bin wani mai laifi a jihar arewa (bidiyo)


Jami’an hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa (DRTS) da aka fi sani da VIO, sun samu raunuka daban-daban a wani hatsarin da suka yi a gadar Lugbe da ke kan titin filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe a Abuja. Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

Hatsarin wanda ya faru da misalin karfe 3:10 na yammacin ranar Litinin, 19 ga watan Satumba, jami’an VIO ne da ke tuki a kan “Hanya Daya” su ka yi taho mu gama da wata mota a mahadar Lugbe.

An tattaro cewa jami’an na tukin mota ne a kan gadar a kokarin da suke na cafke wani direban da ake zargin takardar motarsa ​​ta kare amma ana cikin haka ne suka yi karo da wata mota kirar Toyota Corolla da ke tahowa mai lamba ABJ 717. CE.

An garzaya da jami’an VIO da suka jikkata zuwa asibiti. Motocin biyu da abin ya shafa sun lalace ba za a iya gane su ba.

Lamarin da ya janyo hankulan dimbin masu wucewa da kuma jama’a da suka yi tururuwa zuwa wurin, sun zargi jami’an da haddasa hatsarin.

Direban motar (Ibrahim) wanda ya tsallake rijiya da baya a lokacin da yake bada labarin abin da ya faru da shi ya ce yana hawan gadar ne kwatsam ya ga motar VIO ta taho daga wani bangare da sauri.

Ya ce Allah ne ya raya shi duba da irin illar da hatsarin ya yi.

Latsa kasa ka kalli bidiyo

https://mobile.facebook.com/story.php?story_fbid=481660463822078&id=100013148410557&_rdr

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN