Gwamnatin jihar Zamfara ta ware N500m don rabawa marasa galihu

Gwamnatin jihar Zamfara ta ware N500m don rabawa marasa galihu

Gwamna Bello Matawalle

Gwamnatin Zamfara ta ce ta ware Naira miliyan 500 domin rabawa marasa galihu 50,000 duk wata
.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Alhaji Ibrahim Dosara ya fitar a Gusau ranar Lahadi. Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito.

“Za a raba Naira miliyan 500 ga masu cin gajiyar 50,000 duk wata don taimaka musu wajen tinkarar kalubalen da ake fuskanta a lokacin, da nufin habaka tattalin arzikin jihar,” inji shi.

Gwamnatin ta ce za a ba kowane mai cin gajiyar tallafin N10,000 duk wata, a fadin kananan hukumomi 14.

 Ta ce adadin na daga cikin kokarin sake farfado da shirin rage radadin talauci a jihar.

“Gwamnati ta fitar da karin kudaden don rabawa masu karamin karfi da marasa galihu, duk wata a fadin kananan hukumomi 14 na jihar.

“Wannan baya ga sauran matakan tallafi na gwamnati kamar Naira 20,000 da ake rabawa mata 1,800 duk wata a fadin jihar;

Gwamnatin ta ce shirye-shiryen bayar da agajin za su rage wahalhalun tattalin arziki da ake fama da su, tare da kalubalen tsaro da ke addabar jihar.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN