Gwamna Zulum ya amince da tallafin N10m, gida da karatu ga iyalan kwamandan CJTF da Boko Haram suka kashe a Borno


Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya amince da sakin Naira miliyan 10 da gida ga iyalan Babagana Mallam Tela, kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Civilian Task Force, CJTF, da ‘yan ta’addar Boko Haram suka kashe. Shafin isyaku.com ya samo.

Tela, wanda kuma ake kiransa da “Kadau” a matsayin kwamandan CJTF a Bama, daya daga cikin al’ummomin da aka kwato a Borno, kafin Boko Haram su kashe shi a watan Yuni, 2022.

Civilian JTF' wata fitacciyar kungiyar sa kai ce ta matasa masu shirye-shiryen yaki, wadanda suka shahara wajen amfani da fahimtarsu na yankin Borno wajen yakar 'yan ta'addar Boko Haram da ISWAP.

Wata sanarwa a ranar Asabar, 10 ga Satumba, 2022, a Maiduguri ta hannun mai ba Gwamna shawara na musamman kan harkokin sadarwa da dabaru, Isa Gusau, ta ce Zulum, wanda ya ziyarci iyalan mamacin a Bama, ya kuma amince da bayar da tallafin karatu ga ‘ya’yan marigayin.

Sanarwar ta kara da cewa, "Gwamnan ya bayar da umarnin a fitar da naira miliyan 10 domin kula da iyali na tsawon wani lokaci, ya umarce su da su bude asusu tare da masu sa hannun hadin guiwa, inda za a ba da kudaden." 

“Zulum ya kuma bayar da umarnin a saya wa iyalan Kadau wani gida na Naira miliyan 10 domin su daina biyan kudin haya.

“Zulum ya kuma bayar da umarnin a baiwa ‘ya’yan marigayi kwamandan tallafin karatu na Gwamnatin jihar a duk tsawon karatunsu.

"Gwamnan ya bayyana hakan a matsayin 'karamin tukuicin' saboda gudunmawar da ya bayar wajen samar da zaman lafiya a Bama, Borno da kuma Najeriya baki daya." 

Ya kara da cewa Gwamnan ya kuma bayar da gudummawar kudi da kayan abinci da kayan masaku ga masu aikin sa kai 683 da ke aikin yakar ta’addanci a jihar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN