Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sako karin mutum 5 daga fasinjojin jirgin kasa Abuja-Kaduna


Yanzu muke samun rahoton da ke cewam an sake sakin wasu fasinjoji biyar da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna. Shafin Isyaku News Online (isyaku.com) ya samo.

Legit.ng ta ruwaito cewa ya zuwa yanzu, an sako akalla mutane 37, wanda kuma har yanzu akwai sauran 35 da ke tsare a hannun 'yan bindiga, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

Daga cikin fasinjojin da aka saki akwai Farfesa Mustapha Umar Imam, likita a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodio (UDUS), Sokoto. 

Rahoton Daily Trust ya ce an harbi Farfesa Imam a lokacin da yake, lamarin da ya haifar da damuwa game da lafiyarsa.

Sauran fasinjojin da aka sako sun hada da Akibu Lawal, Abubakar Ahmed Rufai, Muktar Shuaibu da Sidi Aminu Sharif.

Mawallafin jarida a Kaduna, Tukur Mamu, wanda da kansa ya shiga tattaunawar don ganin an sako mutanen amma ya ja baya saboda wata barazana, ya tabbatar da sakin su a ranar Talata 

Kawo yanzu dai babu tabbas ko an biya kudin fansa ga 'yan bindigan.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN