An tattaro cewa lamarin ya faru ne a mahadar Umuikaa, daura da hanyar Fatakwal - Aba - Enugu Expressway a ranar Talata, 16 ga watan Agusta.
Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa Vanguard cewa an samu rashin jituwa tsakanin jami’an hukumar ta FRSC biyu da direban motar, wanda ya kai ga fada. A cikin rudanin da aka samu, daya daga cikin jami’an hukumar FRSC ya caka wa direban wuka a bayansa.
Jami’an FRSC sun kai direban asibitin Ronald da ke Mkpuka, inda Likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Anyatonwu a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Enyinnaya Standhope Nwaigwe ya fitar, ya bukaci kwamandan hukumar FRSC na jihar da ya gaggauta binciki lamarin tare da damke wadanda suka aikata laifin.