Gwamna Abubakar Bagudu na jihar Kebbi, ya amince da nadin Hakimai 12 a kananan hukumomi tara na jihar. Shafin Isyaku News isyaku.com ya samo.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi da Masarautu, Muhammed Sani-Umar ya fitar ranar Talata a Birnin Kebbi.
Sani-Umar ya nakalto Gwamnan yana taya hakiman gundumomi murna tare da yi musu fatan Allah ya yi musu jagora da kuma kariya a kan sabon aikin da aka dora musu. Kampanin dillancin labarai na Najeriya NAN ta ruwaito.