Yan bindiga sun yi awon gaba da wani Kwamishina daga gidansa da karfin tsiya bayan harbe-harbe da bindiga a jihar Arewa


Yan bindiga sun yi awon gaba da Kwamishinan yada labarai da aladu na jihar Nassarawa Mr Yakubu Lawal a cikin daren ranar Litinin. Shafin Isyaku News isyaku.com ya samo.

Rahotanni na cewa yan bindigan sun dira gidan Kwamishinan da ke Nassarawa Eggon da misalin karfe 8:45 na daren Litinin suka fara harbe-harbe da bindiga.

Lamari da ya ja hankalin Yan sanda da ke sintiri kuma suka kai dauki da gaggawa. Sai dai kafin su isa wajen Yan bindigan sun yi awon gaba da Kwamishinan da karfin tsiya.

Kakakin hukumar Yan sandan jihar Nassarawa Nasir, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata takarda da aka raba wa manema labarai.

Kazalika shugaban karamar hukumar Nassarawa Eggon Mr Danlami Idris, ya ce Majalisarsa za ta kara tsaurara matakan tsaro domin dakile ayyukan miyagu da ya haddasa tsoro a zukatan al'ummar karamar hukumar kawo yanzu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN