Tsohon Sarkin Zurmi na jihar Zamfara Abubakar Atiku ya rasu a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Atiku ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Ku tuna cewa an tsige marigayin ne tare da Sarkin Dansadau, Husaini Umar a ranar 27 ga Afrilu, 2021, bisa zargin taimakawa ‘yan fashi a masarautun su .
Wani dan uwa mai suna Sani Zurmi, wanda ya tabbatar wa jaridar Punch cewa har yanzu ba a kawo gawar zuwa Najeriya domin binnewa ba.
“Har yanzu gawarsa tana Dubai saboda rashin samun jirgin da zai dawo da marigayin gida domin yi masa jana’iza,” in ji Zurmi.