Ibtila'in hatsari: Mutane 3 sun mutu, 15 sun jikkata a wani hatsarin mota a Arewa


Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane uku, yayin da wasu 15 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku a karamar hukumar Takai. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Lahadi a Kano.

Ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar.

Abdullahi ya ce, “mun samu daukin gaggawa daga tasharmu da ke Takai da misalin karfe 01:14 na rana daga wani mai suna Muhammad Adamu cewa wata motar bas ta Hummer ta kone kurmus.

“Bayan samun labarin, mun yi gaggawar aika da tawagarmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 01:18 na rana domin kashe wutar.

“Da isowarmu, sai muka gano cewa wata mota ce ta kasuwanci (Hummer Bus) tana jigilar mutane 15, ba tare da lambar rajista ba, daga Kano.

“Ta yi karo da wata mota kirar Toyota Hilux dauke da mutane uku da suka fito daga Jigawa mai lamba JMK 142 XA,” inji shi.

Abdullahi ya ce gobara ta kone motar bas din Hummer.

Ya kara da cewa: “A cikin mutane 18 da lamarin ya shafa, an ceto mutane 15 da ransu sun samu kananan raunuka, yayin da uku daga cikin fasinjojin da ke cikin motar bus din aka ceto su a sume.

“Nan da nan muka mika su da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Takai inda likitocin da ke aiki suka tabbatar da mutuwar mutane uku da suka suma.”

Abdullahi ya ce mutanen uku da aka tabbatar sun mutu sun hada da: Sani Isah mai shekaru 28 da Shamawilu Isah mai shekaru 30 da kuma Musa Yusuf mai shekaru 32.

Ya ce musabbabin faruwar lamarin na da nassaba da hatsarin tukin ganganci tuki.

Jami’in hulda da jama’a ya bukaci masu ababen hawa a ko da yaushe su rika tukin mota tare da yin taka-tsantsan don gujewa abubuwan da ba a zata ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN