Yan bindiga sun sace dalibar UDUTH a hanyar Sokoto zuwa Shinkafi


Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wata dalibar Makarantar koyon aikin jinya da ungozoma da ke Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Danfodiyo (UDUTH) Sokoto. Shafin isyaku.com ya samo.

An tattaro cewa wacce aka kama mai suna Zahra Umar, an yi garkuwa da ita ne a hanyar Sokoto zuwa Shinkafi a ranar Asabar, 30 ga Yuli, 2022. 

Wani ma’abucin Facebook, Abdul-Rahman Geto, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, 1 ga watan Agusta, ya ce masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalanta inda suka bukaci a biya su N30m kudin fansa amma daga baya sun mayar da shi zuwa miliyan uku bayan tattaunawa. 

Ya ruwaito cewa:

“Yan bindiga sun sace wannan yarinya zahra a hanyar Sokoto zuwa Shinkafi ranar Asabar, daliba ce a UDUTH sokoto, a ranar Asabar din da ta gabata ne suka nemi kudin fansa Naira miliyan 30, amma a jiya bayan sun dauki tsawon lokaci suna tattaunawa sun mauar da kudin Naira miliyan 3, ina rokon Allah Ya sa ta dace, ta dawo da 'yancinta da wuri-wuri." ya rubuta.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE