An yi wa wasu mata 8 fyade a fili yayin da suke daukar fim na wakoki


An kama mutane sittin da biyar da ake zargi bayan da aka yi wa mata takwas fyade da yawa tare da yi musu fashi, tare da wasu ma'aikatan kamfanin da ke aiki a wani faifan bidiyon waka a lardin Gauteng na Afirka ta Kudu. Kafar labarai na Isyaku News Online (isyaku.com) ya samo.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 28 ga watan Yuli, a kauyen West, Krugersdorp, lokacin da ma’aikatan tawagar da ke yin faifan bidiyo na wakar bishara, wasu masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, da aka fi sani da zama zamas, suka kai musu hari, a lokacin da suke daukar fim a ma’adanan. 

Ofishin Jakadancin Najeriya a Afirka ta Kudu a wata sanarwa a ranar Litinin, 1 ga watan Agusta, ya ce wani kamfani mallakin Najeriya ne ke da hannu wajen shirya wakokin. 

A yayin faruwar lamarin, an yi zargin cewa masu hakar ma'adinan ba bisa ka'ida ba sun umurci ma'aikatan rawagar da su kwanta yayin da suke bincike.

Zama zama sun busa alamar da ya sa wasu mazaje kusan 10 sanye da barguna na Basotho suka zo wajen. 

Daga nan ne ake zargin ’yan kungiyar sun fara daukar matan daya bayan daya inda suka yi musu fyade a budadden fili.


An yi imanin cewa an ci gaba da hakan sau da dama yayin da ake zargin ma’aikatan tawagar suma an yi musu fashin tufafi, wayoyin salula, kayan ado, jakunkuna, kayan aiki da sauran kayayyaki masu daraja, wanda aka kiyasta kudinsu ya kai Naira miliyan 1.5.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Birgediya Brenda Muridili, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ma’aikatan tawagar mutane 22 – mata 12, masu shekaru tsakanin 19 zuwa 39, da maza 10 – suna daukar wani faifan bidiyo na waka lokacin da wasu mutane sanye da barguna suka kai musu hari. 

Muridili ya ce an kaddamar da wani samame karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda na lardin Gauteng, Laftanar Janar Elias Mawela, a ranar Juma’a, 29 ga watan Yuli, bayan faruwar lamarin.

An harbe wasu mutane biyu a harin bayan sun yi zargin suna nuna bindigogi ga ‘yan sanda yayin da daya ke karbar magani sakamakon harbin bindiga. 

An gano bindigogi biyu marasa lasisi da bama-bamai, tare da kayayyakin da aka sace daga wadanda abin ya shafa. 

Ana sa ran wadanda ake zargin za su bayyana a kotun Majistare ta Krugersdorp a ranar Litinin 1 ga watan Agusta. . 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN