Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani jami’in soji mai suna Manjo Churchill Orji a jihar Anambra. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
An tattaro cewa an kashe sojan ne a ranar Asabar, 20 ga watan Agusta, a wani samame da aka yi a yankin Aziya mai fama da rikici, a karamar hukumar Ihiala ta jihar.
Wani abokin makarantar marigayin, Leonard Edu, ya tabbatar wa jaridar Nigerian Tribune.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Anambra, DSP Ikenga Tochukwu, da aka tuntube shi ta wayar tarho, ya ce har yanzu bai samu rahoton faruwar lamarin ba.