Yadda mahaifi ya dinga yin lalata da diyarsa, ya gayyato mutane 5 yana karbar kudi domin saduwa da diyarsa


Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani mutum mai shekaru 49 mai suna Amoda Bola a ranar 17 ga watan Agusta bisa zarginsa da yi wa ‘yarsa mai shekaru 14 ciki (An sakaya sunanta). Shafin isyaku.com ya samo.

Wanda ake zargin, mazaunin unguwar Idi Oro ne, Ode Remo, an kama shi ne biyo bayan korafin da aka samu daga diyarsa, inda ta bayyana a hedikwatar yan sanda ta Ode Remo cewa mahaifinta da suke zaune tare da ita tsawon wasu shekaru a yanzu yana aikata lalata da ita.

Ta ci gaba da cewa mahaifinta ya kuma rika gayyatar maza zuwa gidan domin yin lalata da ita daga nan ne mazan za su biya shi kudi.

Bayan rahoton, DPO na ofishin Yan sanda na Ode Remo CSP Olayemi Fasogbon, ya jagoranci jami'an yan sanda zuwa wurin, kuma aka kama wanda ake zargin ba tare da bata lokaci ba. 

A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin, wanda ya fara musanta zargin daga baya ya amsa laifinsa lokacin da diyarsa ta fuskance shi. Wannan ikirari nasa ya kai ga kama wasu mutane biyar da suka yi lalata da diyarsa a lokuta daban-daban bisa gayyatar mahaifin.

Wadanda ake zargin sune; Ahmed Ogunkoya 30, Muyiwa Adeoye 48, David Sunday Solaja 69, Emmanuel Olusanya 50 da Joshua Olaniran 50yrs.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi, ya ce dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifin yin lalata da yarinyar ‘yar shekara 14 da haihuwa, kuma sun biya kudi ga mahaifin. Ya ce yarinyar, wadda mahaifiyarta ta rabu da mahaifinta shekaru da suka gabata, ta ce kusan mahaifinta ya mayar da ita karuwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN