Matar tsohon Ministan gida na karkokin waje na Najeriya, Prof. Nicholas Ada ta mutu a hatsarin mota a kan hanyar Gboko zuwa Makurdi ranar Lahadi. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Benue daily post ta ruwaito cewa Shaidangani da ido ya ce hatsarin ya auku ne a garin Tarhembe kuma sakamakon haka matar da direbanta sun mutu nan take.
Rundunar Yan sandan jihar Benue bata fitar da bayani ba dangane da lamarin kawo lokacin rubuta wannan rahotu.