Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane biyar na iyalan Farfesa Ango Abdullahi da wasu a Kaduna


Wasu ‘yan bindiga sun sace wata mata da ‘ya’yanta hudu da sauran su a karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna.

Matar ita ce surukar Hakimin Yakawada, Alhaji Rilwanu Saidu, wanda kane ne ga Shugaban kungiyar Dattawan Arewa (NEF), Farfesa Ango Abdullahi.

Lamarin na zuwa ne makonni kadan bayan dan Farfesa Abdullahi, Sadiq Abdullahi, ya sake samun ’yancinsa bayan kusan watanni hudu a tsare.

Ku tuna cewa ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da Sadiq Abdullahi, da wasu mutum 61 wadanda suka kai hari kan wani jirgin kasa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris.

Wani makusancin dangin Umar Sani wanda ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels afkuwar lamarin, ya ce an sace matar mai suna Ramatu Samaila tare da ‘ya’yanta daga gidansu a yayin harin da aka kai a daren ranar Talata, 9 ga watan Agusta. 

Ya ce ‘yan bindigar da yawan su sun kai farmaki kauyen Yakawada inda suka fara harbe-harbe ba da dadewa ba kafin suka koma gidan hakimin kauyen.

‘Yan bindigar sun kuma yi garkuwa da wasu mazauna garin da suka hada da Abubakar Mijinyawa daya da matansa biyu, Aisha da Hajara.

Rahotanni sun bayyana cewa an tafi da matan biyu wadanda dukkansu mata masu shayarwa ne tare da jariransu yayin da maharan suka kashe wani dan sintiri na yankin mai suna Aminu Lawal a yayin harin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN