"Barayi” sun sace N31m a gidan Gwamnatin jihar Katsina


Wasu da ake zargin barayi ne sun shiga gidan Gwamnatin jihar Katsina inda suka yi awon gaba da Naira miliyan 31 a ranar 31 ga watan Yuli. Shafin labarai na Isyaku News Online isyaku.com ya samo.

Wata majiya mai karfi ta Gwamnati wacce ta tabbatar wa Premiumtimes hakan, ta ce wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kutsa cikin ofishin mai kula da harkokin kudi na gidan Gwamnati inda suka kwashe kudaden da aka ajiye a cikin buhu. Majiyar ta kara da cewa an yi satar ne da daddare lokacin da mai kula da harkokin kudi Salisu Batsari yake ofishin.

"Ban ga hoton CCTV ba amma kun san zai kasance cikin abin da 'yan sanda za su nema. Amma na ji cewa faifan bidiyon sun nuna wani mutum sanye da abin rufe fuska yana shiga ofis ta taga," in ji shi.

Wani mai taimaka wa Gwamnan kan harkokin yada labarai Al Amin Isa ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ki bayar da cikakken bayani kan kudaden da aka sace.

"An kai rahoton lamarin ga 'yan sanda kuma ana gudanar da bincike," in ji sh

Mista Isa ya kara da cewa Gwamnatin jihar da ‘yan sanda suna gudanar da bincike kan satar, kuma za a hukunta wadanda suka aikata laifin. Ya ce lokacin da aka yi satar farko, Gwamnati ta dauki matakin dakile sake afkuwar lamarin amma “kun san yadda wadannan mutane za su iya zama masu wayo.

Majiyar Gwamnatin da ta nemi a sakaya sunanta ta ce an kama wasu jami’ai dangane da faruwar lamarin amma daga baya aka sake su.

“Ranar Litinin da ta gabata Gwamnatin jihar ta samu labarin satar, nan take aka sanar da ‘yan sanda kuma aka fara bincike. ‘Yan sanda sun gayyaci FC (financial controller) da wasu daga cikin ma’aikatansa da kuma wasu jami’an tsaro da suke bakin aiki a ranar da lamarin ya faru ‘yan sanda sun gayyace su domin amsa tambayoyi,” inji shi.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ake samun irin wannan satar a gidan Gwamnatin jihar Katsina. A shekarar 2020, an ce an sace N16m daga ofishin sakataren Gwamnatin jihar (SSG). An kama wasu jami’an Gwamnati biyu a ofishin SSG da wani mai gadi da laifin satar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN