Wasu da ake zargi yan bindiga ne suka kai hari kauyen Buwade a karamar hukumar Illela na Jihar Sokoto kuma an rahoto sun kashe mutum 11, Daily Trust ta rahoto.
Tsohon shugaban karamar hukumar, Abdullahi Haruna Illela, wanda ya tabbatar da harin, ya kuma ce yan bindigan sun sace mutane da dama a kauyukan Buwade da Dambo.
A cewar Haruna, yan bindigan sun afka wa garin na Buwade misalin karfe 8 na daren Talata 'jim kadan bayan sallar Isha'i suka fara harbe-harbe'.
"An tabbatar mutane 11 sun mutu yayin da wasu da dama sun jikkata. Mutane sun tsere daga kauyukan biyu da ke kusa da juna.
"Wasu mazauna garin sun tsere garin Illela, wasu sun tafi Gwadabawa yayin da wasu kuma yanzu suna Sokoto," in ji shi.
Tsohon shugaban karamar hukumar, amma, ya ce bai da masaniya kan harin da aka kai tsohuwar kasuwar kasa da kasa ta Illela.
"Ban ji labarin faruwar lamarin ba amma na san an sace shanu daga kauyuka biyu da suka kai hari," in ji shi.
Martanin rundunar yan sanda
Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar yan sandan Sokoto, DSP Sanusi Abubakar, ya yi alkawarin zai kira amma bai yi hakan ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.