Matan ’yan sanda sun yi azumi da addu’ar Allah kiyaye kada ‘yan bindiga su kashe mazajensu


Matan jami’an ‘yan sanda sun roki Allah kada ya bar ‘yan bindiga su kashe mazajensu saboda halin rashin tsaro da Najeriya ke ci gaba da yi.

Kungiyar matan jami’an ‘yan sanda (POWA) a Kaduna ta ce sun gudanar da taron addu’o’i da azumi na kwanaki biyu suna neman taimakon Allah wajen kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga da Boko Haram.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Mohammed Jalige ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 5 ga watan Agusta a Kaduna.

Mista Jalige ya ce a ranar Alhamis din da ta gabata ne kungiyar POWA reshen Kaduna ta kammala addu’o’i da azumin kwanaki biyu karkashin jagorancin shugabar POWA kuma uwargidan kwamishinan ‘yan sandan, Salimat Ayoku.

Sanarwar ta ce "An yi addu'o'i da kuma zaman azumi don tabbatar da zaman lafiya a Najeriya saboda kalubalen tsaro da aka fuskanta a baya-bayan nan."

“Shugaban POWA, matar babban sufeton ‘yan sanda, Hajiya Hajara Usman, sai da ta umurci ‘yan kungiyar ta POWA da su yi azumi da addu’o’i na kwanaki biyu domin neman taimakon Allah,” in ji ‘yan sandan.

Matan ‘yan sandan sun yi addu’ar Allah ya kawo mana karshen rashin tsaro a Kaduna da Najeriya.

“Sun kuma roki Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da kare ma’auratan su ya kuma ba su nasara a kan makiyan Nijeriya a kowane irin salo a yayin gudanar da ayyukansu,” in ji sanarwar ‘yan sandan.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN