Mukaddashin Kwanturola-Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Mista Idris Jere, ya ce ana shirin daukar karin ma’aikata 5,000 a ma’aikatar. Shafin isyaku.com ya samo.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ta ruwaito cewa Jere, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa da tambayoyi daga manema labarai a Dutse ranar Asabar, ya ce an dauki matakin ne da nufin magance matsalar karancin ma’aikata a hukumar NIS.
“Game da rashin isassun ma’aikata a NIS, kamar yadda kuka sani, yanzu mun kammala daukar ma’aikata kuma muna horar da wadanda aka dauka a yanzu.
“Kamar yadda kuka sani, gwamnati ta sanya takunkumin daukar ma’aikata, amma ta dage hakan a kan jami’an tsaro, domin tsaro shi ne muhimmin abu.
"Don haka, mun rubuta wa shugaban kasa kuma ina da tabbacin za mu samu amincewar daukar karin ma'aikata kusan 5,000 a cikin NIS," in ji Jere.