Kwamishina a Sokoto, Shugaban karamar hukuma da wasu da dama sun fice daga PDP zuwa APC


Shugaban karamar hukumar Tangaza da kansilolinsa shida, jigo a jam’iyyar People Democratic Party (PDP), Kanar Garba Moyi (rtd) sun fice daga jam’iyyar adawa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress. Shafin isyaku.com ya samo.

Moyi wanda yana daya daga cikin kwamishinonin da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya sake nada a kwanakin baya bayan ya sake nada Majalisar zartarwar jihar Sokoto, ya taba zama tsohon kwamishinan tsaro kafin ya bar takarar tikitin PDP na shiyyar Sanatan Sokoto ta Gabas.

Daily trust ta ruwaito cewa tsohon Kwamishinan ya samu tarbar shugaban jam’iyyar APC na Sakkwato kuma Sanata mai wakiltar Sokoto-Arewa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da mataimakin dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC, Injiniya Idris Gobir a gidan Wamakko da misalin karfe 9 na daren Lahadi. 

Kansilolin da suka sauya sheka sun hada da Zakariyya Madugu, Abubakar Abubakar Kalanjine, Abubakar Aliyu, Halilu Aliyu, Ibrahim Sarkin Tudu da Musa Sulaiman Sakkwai.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN