Buhari: Da zarar an yi kidaya a 2023, za a samu mafita ga matsalar rashin tsaro


A ranar Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana fatansa na cewa kidayar jama’a ta 2023 za ta taimaka wajen yaki da matsalar rashin tsaro da ke addabar Najeriya.

Bayanin na Buhari ya fito ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar, Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ce Buhari ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki na kasa kan kidayar yawan 'yan Najeriya da gidajensu na 2023 da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja.

Buhari ya jaddada cewa fasahar zamani za ta tabbatar da cewa bayanan kidayar sun fito da inganci kuma a yi amfani dasu yadda ya dace.

Ya kamata a yi kidaya tun tuni, inji Buhari

Ya bayyana takaicin cewa ba a gudanar da kidayar al’ummar Najeriya ba bisa ka’ida a duk bayan shekaru 10 kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ba da shawara.

An yi kidayar jama’ar Najeriya ne 2006, shekaru 16 kenan akalla da suka gabata.

Shugaba Buhari ya ce kidayar 2006 ta riga ta wargaje, wannan yasa bayanan yawan 'yan Najeriya ke da shi a ma'adar bayanai, rahoton Channels Tv.

Don haka shugaban ya bukaci goyon bayan masu ruwa da tsaki da suka hada da Gwamnatocin Jihohi, Majalisun Kananan Hukumomi, bangaren Gargajiya da Addini da sauran jama’a domin samun nasarar gudanar da ayyukan kidayar ta 2023.

A nasa jawabin, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya tabbatar da kalaman na Buhari tun da farko yana mai cewa duba da yanayin karuwar yawan al’umma na 2.3% bisa dari, Najeriya za ta kasance kasa ta uku mafi yawan jama'a a duniya nan da 2050.

Abin na yi ne: Za a dauki mutane miliyan 1 aiki a 2023 domin a gano yawan 'Yan Najeriya

A shirin yin wannan kidaya, hukumar NPC ta kasa, ta ce mutane miliyan daya za a dauka aiki domin taimakawa gwamnatin tarayya a kidayar da za a yi a shekara mai zuwa.

Daily Trust ta rahoto hukumar tarayyar ta na cewa za ayi amfani da fasaha na zamani wajen aikin kidayar domin hana ‘yan siyasa da sauran manya yin coge.

Sanannen abu ne cewa ana zargin wasu su kan kara yawan mutane idan aka tashi kirga adadin yawan al’umma, ana yin haka ne domin cin ma wata manufa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN