Kebbi: An zartar da hukuncin bulala 40 ga matashin da Kotu ta kama da laifin neman matar aure (Hotuna)


Jami'an sashen shari'a a jihar Kebbi sun zartar da hukuncin bulala 40 kan Mubarak Lawali a garin Kamba. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Biyo bayan kama Mubarak Lawali da laifin neman matar aure da niyyar yin lalata da ita ranar Talata 30 ga watan Agusta, Kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekara 2 a Kurkuku. Zai kuma biya tarar N50.000 da kuma biyan diyyar N50.000 ga wanda ya shigar da kara, sai Kuma bulala 40 da za a yi masa a bainar jama'a .

Sakamakon haka an zartar da hukuncin a ranar Laraba 31 ga watan Agusta a Tashar Garba da ke garin Kamba. Mubarak ya kwanta a kan benci kuma aka zartar masa da hukuncin bulala 40 sakamakon umarnin hukuncin Kotu.

Wata majiya da bata son a ambaci sunanta, ta shaida mana cewa, an tasa keyar Mubarak zuwa Kurkuku domin fara zaman gyara hali na tsawon shekara 2.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN