Hotunan jana'izar wasu 'yan uwa guda bakwai da suka rasu bayan cin karin kumallo a Sokoto


Mata biyu da ‘ya’ya biyar na wani mutum mai suna Malam Danbala sun mutu bayan sun ci karin kumallo a kauyen Kaura da ke karamar hukumar Yabo a jihar Sakkwato. Shafin isyaku.com ya samo.

An yi jana’izar wadanda suka mutu a ranar Talata 30 ga watan Agusta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. 

Danbala ya ce matsalar ta samo asali ne lokacin da daya daga cikin matansa ta dafa wani abincin gida mai suna Dambu ​​domin yin karin kumallo.

“Dukansu sun ci abinci sun gamsu, bayan wani lokaci suka fara korafin ciwon ciki, aka garzaya da su asibiti, yaran biyar sun fara rasuwa, sai mata na suka rasu da tsakar dare amma yarinyata ta na karbar magani " in ji shi.

A cewar wani shaidar gani da ido, matar ta fara dafa abincin dare ne a ranar Lahadi da ta raba da makwabta.

“An ce ragowar abincin an ajiye su ne domin yin karin kumallo, kuma a safiyar ranar Litinin ta hada ragowar abincin da danyen Dambu ​​da aka ce ba a gano ba har tsawon dare.''

“Haka ne Allah ya kaddara musu makomarsu, Allah ya ba su Jannatul Firdaus,” shugaban iyalan ya kara da cewa.Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN