Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya amince da sakin naira miliyan goma sha bakwai da dubu dari hudu a matsayin tallafin kudi ga matasa yan jihar Kebbi masu zuwa horo kan aikin soja da na kaki gaba daya. Shafin Isyaku News Online isyaku.com ya samo.
Amincewar na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin shugaban ma’aikata na jihar Kebbi, Alhaji Safiyanu Garba Bena kuma aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi a ranar Litinin din nan.
A cewar sanarwar, jimillar matasa 369 ‘yan asalin jihar Kebbi ne za su je domin samun horon ‘yan sandan Najeriya a matsayin ‘yan sanda, ‘Direct Short Service da Direct Combatant Commission of the Nigerian Army, da kuma gudanar da aikin daukar ma’aikata a shekarar 2022. Da Kuma wadanda suka shiga Rundunar Sojan Sama ta Najeriya a matsayin Airmen /AirWomen.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, matakin da Gwamna Bagudu ya yi na da nufin rage zaman kashe wando a tsakanin matasa masu tada zaune tsaye a jihar, da kuma kudurin wannan gwamnati na cike kason jihar yadda ya kamata a yankunan da aka ambata