Hukumar soji ta kafa kwamitin da zai binciki kisan Sheikh Goni a Yobe


Hedkwatar sashi na 2 na Rundunar Operation Haɗin Kai ta hukumar sojin Najeriya ta kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan zargin hannun wasu sojoji a kisan Sheikh Goni Gashua a jihar Yobe.

Legit.ng ta ruwaito cewa a wata sanarwa da ta fitar ta hannun ɗaya daga cikin kakakinta, Kaftin Kennedy Anyanwu, hukumar sojin ta ce a halin yanzun tana kan bincike don gano cikakkun bayanan Sojojin

Jaridar Premium Times ta ruwaito yadda aka cafke Sojoji biyu bisa zargin kisan babban Malamin addinin Musuluncin.

Sheikh Goni ya rasa rayuwarsa ne hannun wasu mutane a kusa da Jaji Maji, ƙaramar hukumar Karasuwa a jihar Yobe, ranar Jummu'a da daddare.

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Yobe, Dungus Abdulkareem, wanda ya tabbatar da lamarin ga jaridar, ya ce, "Nan da ƴan kwanaki za'a bayyana cikakken abun da ya faru ga al'umma."

Wane mataki hukumar Sojojin Najeriya ta ɗauka?

Da take tabbatar da lamarin, rundunar Sojin Najeriya ta ayyana kisan Malamin da babban abun takaici da dana sani, "Duk da rashin sassauci kan take doka da ƙa'idojin aikin soji."

A sanarwan da ta fitar ranar Lahadi, Rundunar sojin ta ce:

"Sashin sojin tare da haɗin guiwar hukumar yan sanda reshen jihar Yobe sun duƙufa bincike domin gano cikakkun bayanan Sojojin da ake zargi."

"Bugu da kari sashin Sojin ya kafa kwamitin bincine da zai bankaɗo duk wani abu Mai alaƙa da lamarin mara daɗi, kuma daga ƙarshe za'a miƙa Sojojin su fuskanci dokar hukumar soji da ta fararen hula."

Dakarun yan sanda sun kai samame sansanin yan bindiga a kauyen Anguwan Mai Zuma, ƙaramar hukumar Ɗanja a Katsina.

Rundunar yan sanda ta ce yayin samamen, Jami'ai sun sheke ɗan ta'adda ɗaya, sun kwato kayan aikin su da yawa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN