Gwamna Bagudu ya yi jimamin rasuwar shugaban karamar hukumar Zogirma-Tilli

Gwamna Bagudu ya yi jimamin rasuwar shugaban karamar hukumar Zogirma-Tilli


Wata sanarwa dauke da sa hannun Yahaya Sarki, mai baiwa Gwamnan jihar Kebbi shawara na musamman kan harkokin yada labarai (SA) ta ce Gwamna Atiku Bagudu ya jajantawa iyalan marigayi Hon. Shugaban Karamar Hukumar Zogirma-Tilli. Shafin labarai na Isyaku News isyaku.com ya samo
.

Shugaban Majalisar Raya Yankin, Hon. Sambo Sarkin Yaki Zogirma ya rasu ne sakamakon doguwar jinya ranar Juma'a a asibitin koyarwa na Usmanu Danfodio da ke Sokoto.

Gwamnan tare da rakiyar Ministan shari’a kuma babban lauyan tarayya Abubakar Malami SAN da shugaban jam’iyyar APC na jihar Abubakar Muhammad Kana Zuru, sun yi addu’ar Allah ya jikan marigayin ya gafarta masa, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure rashin.

Marigayin mai shekaru 66, ya rasu ya bar mata hudu da ‘ya’ya ashirin. Daga cikin ‘ya’yansa akwai Murtala Sambo Zogirma, Kansila mai wakiltar unguwar Zogirma.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN