
An tsinci jaririyar da aka bari a gefen hanya a Minna
August 24, 2022
Wani ma’abocin Facebook, Comrade Lanre Sadiq, wanda ya wallafa hotunan a safiyar Laraba, 24 ga watan Agusta, ya yi kira ga hukumar da ta dace da ta ceto yaron.
"Rayuwar MACE BAYAN WATA TARA. Hoton da ke kasa sabon jariri ne da aka yi watsi da shi a unguwar Gidan-Mongoro daura da hanyar Bida a cikin garin Minna". ya rubuta.