Zaben Osun: Adeleke na PDP ya doke Gwamna Oyetola na APC a Mazabar gidan gwamnatin Osun


Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya doke Gwamna Gboyega Oyetola na jam’iyyar All Progressives Congress a gidan gwamnatin Osun. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

Adeleke ya samu kuri’u 117 a mazabar Agowande/Oshogbo GRA/ Mazabar gidan Gwamnati, yayin da Oyetola ya samu kuri’u 106.

Mazabar na karamar hukumar Olorunda. Ana ci gaba da kidayar kuri'un da aka kada a zaben Gwamnan jihar da aka gudanar a yau 16 ga watan Yuli. 

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN