Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP),Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.
Baturen zabe a jihar, Toyin Ogundipe, ne ya sanar da sakamakon zaben a safiyar ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, jaridar The Cable ta rahoto.
Adeleke ya samu kuri’u 403, 371 wajen lallasa babban abokin hamayyarsa Gboyega Oyetola na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ya samu kuri’u 375,027.
Dan takarar na PDP ya lashe kananan hukumomi 17 yayin da gwamna mai ci ya samu kananan hukumomi 13 kacal, jaridar Punch ta rahoto.