Type Here to Get Search Results !

Yanzu-Yanzu: Bayan ganawa da Buhari, gwamnonin APC sun fadi matsayarsu kan takarar Tinubu da Shettima


Gwamnonin jam’iyyar APC tara sun yi ganawar sirri ta sa’a daya da shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a ranar Litinin, 11 ga watan Yuli.

A karshen taron, gwamnonin sun bayyana goyon bayansu ga Sanata Kashim Shettima a matsayin dan takarar maaimakin shugaban kasa na jam’iyyar a 2023, inji rahoton jaridar Punch.

Legit.ng ta tattaro cewa gwamnonin sun kuma ce sun amince da hadakar Tinubu da Shettima domin tabbatar da nasarar jam’iyyar mai mulki a zaben shugaban kasa na 2023.

An jiyo shugaban kungiyar gwamnonin na APC Abubakar Bagudu yana cewa:

Mun yi matukar mamakin lokacin da Asiwaju Ahmed Tinubu ya bayyana a Daura ranar Lahadi cewa Sanata Kashim Ibrahim Shettima ne dan takarar mataimakin shugaban kasa.

“Mun yi farin ciki da cewa ba karamin mutum ba ne Sanata Shettima da aka bayyana dan takarar mataimakin shugaban kasa. Babu shakka, Sanata Shettima zai cika kyawawan manufofin Asiwaju Tinubu.

"Mun yi matukar farin ciki da zabin, su biyun za su kara kaimi, kuma za su karfafa nasarorin da shugaban kasa ya samu a cikin shekaru bakwai da suka gabata."

Bagudu ya kara da cewa ziyarar da suka kai Daura sun kai ta ne domin taya shugaban kasar murnar Sallah.

Yadda aka zabo Shettima, inji gwamna Uzodimma

A bangare guda, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, shi ma ya ce zabar Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa shawara ce ta dukkanin gwamnonin APC.

Ya kara da cewa dukkan gwamnonin za su yi aiki tukuru domin ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a zaben 2023.

A kalamansa:

“Zaben Sanata Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa shawara ce ta gama-gari. Za mu yi aiki tukuru don ganin mun samu nasara a dukkan jihohinmu”.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies