Duba abin da Ministan shari'a Abubakar Malami ya ce a gidan Wamakko a Sokoto


Ministan shari’a Abubakar Malami ya bayyana Sen. Aliyu Wamakko (APC-Sokoto ta Arewa), a matsayin uba kuma shugaban siyasa. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

Malami ya yi wadannan kalamai ne yayin da ya kai wa Wamakko ziyarar Sallah a Sokoto ranar Litinin.

NAN ta ruwaito cewa wata sanarwa da mai taimaka wa Wamakko kan harkokin yada labarai, Bashar Abubakar, ya fitar a ranar Talata, ta ce Malami ya bayyana cewa ziyarar alama ce ta girmamawa da biyayya ga tsohon Gwamnan jihar bisa ga al’ada.

Malami ya ci gaba da cewa: “Na zo ne domin in yi murna da ku a matsayinka na uban siyasa, shugabanmu kuma fitaccen Sanata.

"Na yi farin ciki da irin mutanen da na gani a gidanku da suka zo bikin Sallah makamancin haka."

An kuma ruwaito Malami yana mika godiyarsa ga Wamakko bisa sakon ta’aziyyar da ya yi na rasuwar abokansa hudu na tun yaranta.

Ya ce sun mutu ne a ranar Alhamis, a wani mummunan hatsari da ya rutsa da su a hanyarsu ta zuwa jihar Kebbi, daga Abuja, domin bikin Sallah.

Da yake karbar Ministan da tawagarsa, Wamakko ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar abokan Ministan.

Ya bayyana wadanda suka mutu a matsayin masu tawali’u, abokantaka da mutuntawa, yana mai cewa, “rashin da mutuwarsu ta haifar ya yi yawa.”

Wamakko ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta musu dukkan zunubansu, ya kuma baiwa Malami da iyalinsu karfin gwiwa na jure asarar.

Sanatan ya kuma yi amfani da ziyarar wajen taya Ministan murnar kara mata ta uku a cikin iyalansa a ranar 1 ga watan Yuli.

Malam Bashir Gidan-Kanawa ya gabatar da addu’a ta musamman ga wadanda suka rasu yayin ziyarar.

Ministan ya samu rakiyar tsohon mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Bello Magaji da wani babban darakta na hukumar raya kogin Sokoto Rima, Alhaji Faruk Madugu da dai sauransu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN