Yan bindiga sun yi kwantan bauna, sun kashe babban Basarake a jihar Arewa


Wasu mutane dauke da bindigu waɗan da ake zargin 'Yan bindiga ne sun halaka Ibrahim Yamusa, basaraken masarautar Yakuben, cikin karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.

Channels Tv ta samo cewa 'yan bindigan sun halaka matukin sa wanda kuma ya kasance dan sa ne.

Kafin halaka su, 'yan bindigan sun sace basaraken da dan na sa a ranar Alhamis, a wani kwanton bauna da su ka kai musu akan hanyar su ta dawowa daga Takum.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, babban dan basaraken wanda kuma shine magatakardan sa, Fasto John Ibrahim, ya bayyana cewa an yi musu mummunan kisa akan hanyar su ta dawowa zuwa masarautar.

Yan bindiga sun shammaci mahaifina da danuwa na. Sun yanke shawarar tafiya a babur inda suka bar motar sa saboda rashin kyawun hanyoyin mu." A cewar sa.

Basaraken ya shirya halartar wani taron zaman lafiya a Takum, amma ya yanke shawarar dawowa gida saboda an dage taron.

Kakakin riko ta hukumar 'yan sandan jihar Taraba, DSP Kwache Gambo, ta tabbatar da aukuwar lamarin a daren ranar Asabar.

Ta bayyana cewa an gano gawarwakin basaraken da ta dan nasa a cikin wani daji can nesa da wurin da aka sace su.

A cewar Gambo, tuni aka fara bincike domin gano waɗanda ke da hannu akan kisan kamar yadda kwamishinan 'yan sandan jihar ya bada umurni.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN