Yadda yan bindiga suka sace mutane 36 a Kaduna, cikakken rahotu


Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane kusan 36 da suka hada da yara da mata masu shayarwa a unguwar Keke B da ke garin Millennium a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna. Shafin isyaku.com ya samo.

‘Yan fashin sun far wa al’ummar ne da misalin karfe 9 na daren ranar Litinin, 25 ga watan Yuli, lokacin da mazauna gida ke cikin gida sakamakon mamakon ruwan sama.

Wani ganau mai suna Muhammad Salihu ya shaida wa Daily trust cewa ‘yan fashin da suka yi aikin ba tare da kalubalantarsu ba, sun rika shiga gida gida. 

“Da yawa daga cikinmu muna waje lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari saboda da wuri ne, da misalin karfe 8:30 na dare. Sun zo da adadi mai yawa, suna harbi lokaci-lokaci kuma suna rike da muggan makamai,” in ji shi. 

“Sun shiga gidajen mutane daya bayan daya suka yi awon gaba da mutanen, mutum daya mai kanikancin babur ya samu nasarar tserewa daga hannun masu garkuwar, amma sun tafi tare da mazauna 36.” 

Wani ganau ya shaida wa jaridar Tribune cewa mazauna yankin duk sun kasance a cikin gida sakamakon ruwan sama da aka samu tun karfe 7 na dare.

"Ba wanda ya yi tsammanin wani abu sai kawai ya ji karar harbe-harbe. Daga nan ne muka gano cewa wani abu ya lalace." Yace. 

A cewar Yakubu Isa, wani mazaunin yankin, “yanzu mun gano cewa da yawa daga cikin mazauna yankin da suka hada da mata masu shayarwa da jarirai dan shekara biyu sun bace a gida.”

“Yanzu haka mazauna yankin sun fara yin la’akari da irin hasarar da suka yi kamar yadda ku ka ga muna tattara sunayen ne kawai. An yi garkuwa da yawa daga cikin mazauna garin.

An kuma tattaro cewsjamian tsaro sun ziyarci yankin domin duba halin da ake ciki yayin da aka samu kwanciyar hankali a yankin da ma sauran yankunan da ke kewaye.

A halin da ake ciki kuma wani Safiyanu Abdullahi ya ce ‘yan uwansa hudu da suka hada da uwa daya da ‘ya’yanta uku na daga cikin wadanda ‘yan fashin suka yi garkuwa da su. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN