Rahotanni sun bayyana cewa kasar Dubai ta haramtawa ‘yan Najeriya takardar izinin shiga kasar saboda fadan da aka yi a Satwa.
Haramcin ya zo ne bayan wasu bakin haure daga Afirka, tare da wasu ‘yan Najeriya, sun haifar da rudani a kasar UAE.
Bidiyon lamarin ya nuna wasu samari dauke da adduna suna yin barna a unguwar da dare. Sun fasa gilasan wata mota, sun lalata wasu kadarori, sun bi mutanen da ba su ji ba su gani ba, sannan kuma sun kawo cikas ga zaman lafiya a unguwar da babu ruwanta.
Kwanaki bayan da faifan bidiyon ya fara yaduwa, an sanar da cewa ‘yan sandan Dubai sun kama masu da ake zargin tayar da zaune tsaye.
Yanzu dai an ce gwamnatin Dubai ta dauki matakin da ya dace ta hanyar dakile hanyoyin da ‘yan Najeriya ke neman bizar zuwa kasar Dubai.
Wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun ce a halin yanzu hukumomin Dubai ba su ba da biza ga maza 'yan Najeriya ‘yan kasa da shekaru 36 ba.
Look at what Africans are doing in UAE, Ajimaih Dubai. Chai. 💀pic.twitter.com/BTDo6DfSYp
— Aji Bussu Onye Mpiawa azụ 🏳️🌈 (@AfamDeluxo) July 19, 2022
Da yake mayar da martani daga Dubai, dan wasan Najeriya, Aremu Afolayan, ya koka da cewa wannan mataki da mahukuntan Dubai suka dauka zai shafi 'yan Najeriya masu aiki tukuru.
Ya ce ‘yan Najeriya na da ‘yancin zama a Dubai bisa doka kuma ‘yan Najeriyar da ke haddasa rikici a Dubai sun sabawa doka.
“Ku debo masu tayar da hankali kada ku yi amfani da hakan wajen lalata rayuwar kowane dan Najeriya,” in ji shi a wani faifan bidiyo.
Ya kara da cewa kowa dan ci-rani ne a wasu kasashe, don haka ba daidai ba ne a yi wa duk ‘yan Najeriya hukunci bisa ga abin da wasu ‘yan tsiraru suka yi.
Ya kara da cewa, "Suna tada fitina suna kashe juna, suna kai su gidan yari, suna yi musu komai, sun cancanci hakan. Amma akwai 'yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba da ke bukatar ciyar da su."
Ya kuma tambayi abin da jakadan Najeriya a Dubai yake yi na taimakon ‘yan Najeriya da wannan haramcin ya shafa.